Dan wasan gaban Kungiyar kwallon kafan Liverpool Phil coutinho ya samu rauni a karawar da Kungiyar sa tayi da ta Arsenal a ranar 14/08/2016, wanda hakan yasa dole sai da aka chanza shi daga wasan.
Dan wasan dai shine wanda yaci wa kungiyar sa kwallaye biyu a nasarar da Kungiyar sa sukayi a wasan.
Daga gefe guda suma Kungiyar ta Arsenal sun Rasa ‘yan wasan su guda biyu ta sanadiyyar jin raunika da sukayi wato Aaron Ramsey Da kuma Iwobi.
Haryanzu ba’ a tabbatar da iya lokacin da zasu dauka suna jiyya ba.
Liverpool ta samu nasara akan Arsenal a gidanta, wanda nasarar itace ta farko a shekara bakwai (7).