Cutar Amai Da Gudawa Ta Harbi Dalibai 55 A Makarantar Kwana A Kaduna


Cutar amai da gudawa dai ta fara yaduwa a Nijeriya inda a yanzu haka ta bulla a wata makarantar kwana ta ‘yammata mai suna GGSS Kawo a cikin jihar Kaduna, inda ta kashe daliban makarantar guda biyu.

A jiya mujallar Alummata ta rawaito cewa annobar cutar ta barke a wata unguwa a karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa inda ta harbi mutane 20 ya kuma yi sanadiyyar mutuwar wata mata a unguwar

Cutar dai ta kara kamari ne a safiyar ranar Litinin a makarantar inda a yanzu haka kimanin dalibai sama da 50 ne suka kamu da cutar a kuma an garzaya dasu zuwa wani babban asibiti a jihar.

Karanta: Cutar Amai Da Gudawa Ta Barke A Jihar Nasarawa – AREWA24NEWS

Kwamishinan ilimi na jihar, Alh Jafaru Sani, ya tabbatar wa da kafar BBC cewa, kimanin dalibai 55 ne suka kamu da cutar ta kwalara a makarantar.

Alhaji Jafaru ya ce, ba a yi wata-wata ba aka kwashesu aka kai su asibitin Kawo da ke jihar kuma daliba daya ce ta rasu a cikin wadanda suka kamu da cutar, akasin yadda ake rade-rade cewa dalibai biyu ne.

Alhaji Jafaru Sani ya ce, cutar ta bulla ne sakamakon karancin wutar lantarki da aka shafe kwana uku babu a makarantar sai aka rasa ruwa sha dana sauran amfani a makarantar.

Ya ce hakan ya sa daliban suka fara zuwa wata rijiya da ke kusa da wani rafi a kusa da makarantar suna dibar ruwa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like