Gwamnatin jahar Kano ta sanar da barkewar cutar kaji a jahar.
Daraktan sashen kula da dabbobi na ma’aikatar noma da ma’adanai ta jahar Shehu Bawa shi ya bayyana haka ga hukuar yada labara ta kasa (NAN) a ranar Larabar da ta gabata a jahar ta Kano.
Bawa ya bayyana cewa cutar ta barke ne a daya daga cikin manyan gidajen gona da ke jahar.
Ya kara da cewa gwanati na yin ya kokarinta wajen ganin cewa cutar ba ta yadu ba zuwa sauran gidajen gonan.
Daraktan ya kuma yi kira ga masu kiwon kai a jahar da su gaggauta kai rahotan barkewar cutar a gonakin su ga hukuma, domin a dau mataki.