Cutar K’yanda ta barke a sansanin yan gudun hijira dake Benue


Mutane da dama ne suka kamu da cutar kyanda a sansanin yan gudun hijira dake Abagana, wani yanki dake wajen birnin Makurdi.

Wakilin jaridar Daily Trust da ya ziyarci sansanin a ranar Alhamis ya bada rahoton cewa sama da mutane 30 mafi yawancinsu maza da mata su ne suka kamu da cutar.

Daya daga cikinsu mai suna, Sarah Tyohem dake dauke da juna biyu wacce ta bar gidanta dake kauyen Torkula a karamar hukumar Guma bayan wasu yan bindiga sun kai hari kan wani kauye dake kusa da su a ranar sabuwar shekara, ta ce tuni ta fara samun sauki sanadiyar maganin da ake mata.

Tyohem ta ce ko mako daya ba ayi ba da cutar kyanda ta barke a sansanin amma ta yadu cikin sauri a tsakanin  wadanda ke rayuwa a ciki,  ta bayyana godiyarta ga tawagar jami’an kiwon lafiya saboda daukin da suka kai cikin sauri.

Wani jami’i a sansanin wanda yaki yarda ya bayyana sunansa ya yi zargin cewa a kalla mutane hudu ne suka mutu sanadiyar cutar, musamman idan aka yi duba da yanayi na rashin tsabta a sansanin dake dauke da mutane sama da 35,000.

You may also like