Mutane 7 ake fargabar sun mutu ya yin da wasu da dama suke karbar magani bayan barkewar wata cuta da ake zaton cutar Sankarau ce a kauyen Jaja dake mazabar Ganagarawa a karamar hukumar jibia ta jihar Katsina.
An ta garzaya da marasa lafiya ya zuwa Cibiyar Kula Da Lafiya a Matakin Farko dake Jaja domin kula da su.
Wata majiya ta shedawa jaridar Daily Trust cewa tuni shugaban gudanarwa na karamar hukumar, Almustafa Idris ya yi wa iyalan wadanda suka rasu ta’aziya kana aka bada magani ga mutanen da suke kwance a asibiti.
Haka kuma, kusan mutane 104 ne suka kamu da Tarin Fuka a kauyukan, Unguwar Kuka, Kaishemu da Dambawa dake mazabar Bugaje a karamar hukumar ta Jibia.
Da aka tuntubi babban sakatare a ma’aikatar Lafiya ta Jihar, Dakta Kabir Mustafa ya tabbatar da faruwar lamarin kana ya ce tuni suka tura tawagar jami’an lafiya zuwa karamar hukumar.