Cutar zazzaɓin Lassa ta ɓulla jihar Ondo


An samu rahoton ɓullar cutar zazzaɓin Lassa a jihar Ondo.

Dr Liasu Ahmad shugaban Cibiyar Lafiya Ta Tarayya dake Owo shine ya tabbatar da rahoton samun ɓullar cutar ga manema labarai jiya.

Amma kuma Ahmad yaƙi yarda ya yi karin haske inda yace alhakin gwamantin jihar Ondo ne ta fitar da cikakken bayani kan ɓullar cutar.
Wasu mutanen da ake zargin sun kamu da cutar an kwantar da su a cibiyar ya yin da wadanda suke cikin mawuyacin hali aka dauke su zuwa asibitin kwararru dake Irua a jihar Edo.
Haka kuma wani likita dake aiki a cibiyar kula da lafiyar ya tabbatar da cewa an kawo wasu iyalai huɗu asibitin daga yankin Oka-Akoko dake jihar yayin da aka garzayo da wasu mutane 6 da ake zargin sun kamu da cutar daga ƙananan hukumomin Owo da Ose na jihar.

Ya ce likitoci dake aiki a cibiyar suna aiki ne cikin fargabar kamuwa da cutar.

You may also like