Gwamnatin jihar Gombe ta ce cutar zazzaɓin Lassa ta kashe mutum guda a jihar.
Joshua Abubakar, wani darakta a ma’aikatar lafiya ta jihar shine ya tabbatarwa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN haka ranar Litinin a Gombe.
Abubakar yace wata mace mai shekaru 18 wacce aka gwadata tana ɗauke da cutar, ta mutu a ƙaramar hukumar Funakaye.
Amma kuma ya ce an gano matar tana ɗauke da cutar ne bayan da ta mutu.
A cewarsa gwamnati ta tattara sunayen duk wadanda matar tayi mu’amala da su haɗi da ma’aikatan lafiya domin tabbatarwa da hana cutar bazuwa.
Ya shawarci mutane kan su riƙa alkinta abinci a gidajensu domin hana ɓera shiga.
Daraktan ya ƙara da cewa cutar zazzaɓin Lassa ɓera ne yake haddasa ta kuma tana yaɗuwa da sauri da zarar mutum ya haɗa jiki da mai ɗauke da cutar.