Danna hoton sama ku saurari shirin:
Yara rukunin mutane ne masu rauni, kuma akwai wasu cuttuka da suka fi kama su a lokacin hunturu, wadanda ya kamata iyaye mata su kiyaye.
Cututtuka sun hada da wadanda suka shafi hanyoyin shakar iska da cutar sanyi ta nimoniya da mura da tari.
Haka kuma yaran da ke da cutar asma da masu cutar sikila yanayinsu na kara tsananta a wannan lokaci.
Shafin intanet na wikipedia ya bayyana hunturu da cewa, lokaci ne na iska da kura wanda ke kadawa daga Sahara ya bi ta yammacin Afrika, zuwa gabar tekun Guinea.
Wannan yanayi yana kamawa ne daga karshen watan Nuwamba zuwa tsakiyar watan Maris.
Sannan a lokaci ne ake sanyi a mafiya yawan wurare da ke yankin.
Haka zalika a wannan lokaci ne kuma ake hazo.
Kuma akan kwashe tsawon kwanaki ba a ga rana ba.