Dakataccen Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal Ya Bayyana Gaban Kwamitin Bincike


babachir

Dakataccen Sakataren gwamnatin tarayya  Babachir David Lawal ya bayyana gaban kwamitin bincike wanda mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osibanjo yake shugabanta a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.

Lawal ya bayyana ne a gaban kwamitin domin ya kare kansa, kan zargin da ake masa cewa kamfaninsa ya karɓi kwangila ta naira miliyan ɗari biyu(200,000,0000) domin yanke ciyawa a jihar yobe.

A makon da yagabata ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin bincike na mutane uku wanda mataimakinsa Osibanjo yake shugabanta domin ya bincika zarge-zargen da ake wa Babachir da kuma shugaban hukumar leƙen asiri ta ƙasa NIA, Ayo Oke.

An dakatar da Mista Oke ne bayan da hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta gano wasu maƙudan kuɗaɗe a wani gida dake Ikoyi  a jihar Lagos inda hukumar ta NIA tace mallakinta ne.

Tundafari dai kwamitin majalisar dattijai dake kula da aiyukan jinƙai a yankin arewa maso yamma ya samu dakataccen sakataren gwamnatin da laifin saɓa ƙa’ida wajen bada kwangila.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like