Da Ni Aisha Ta Yi Wa Abinda Ta Yi Wa Buhari, Da Tuni Ta Daɗe Da Zama Bazawara A Ɗakin Gyatumarta
Tsohon bulaliyar majalisar dattawa Sanata Rowland Owie, idan matarsa ce ta yi masa abinda Aisha Buhari ta yi wa Mijinta, zai gaggauta kora ta gidan gyatumar ta.
A tattaunawar da ya yi da jaridar Vanguard Sanata Owie ya ce, idan Aisha na da abin faɗa a ɗakin barcin su ya kamata ta bayyana masa ba a ɗakin yaɗa labarai na duniya. “Idan matata ta shiga kafar yaɗa labarai ta tozarta ni cikin awa 24 za ta kanta tana mai tattara komatsanta zuwa gidan tsohon ta”.