Da Alamar APC Zata Fadi A Zaben Kakakin Majalisar Dokoki Ta KasaAna ta kai gwaro ana kai mari a wani yunkuri na fitad da sabbin Shugabanin Majalisar Wakilai.

Abin yana daukan wani salo domin wannan shi ne karo na farko da za a samu Jamiyyu har takwas a majalisar tun dawowa tafarkin damokradiya a shekara 1999. Ko a yanzu masu neman kujerun shugabanci sun fi yawa a Jamiyyar APC mai mulki, saboda haka sai ya nuna alamun rarrabuwar kawuna, kuma wannan shi ne abin da Jamiyyun adawa suka fara kokarin yin amfani da shi, domin su fito da shugaba, duk da cewa har yanzu akwai wadanda ba su da tabbacin kujerun da suka ci saboda inkonklusib a jihohin su.

Yan PDP, LP, APGA, YPP, NNPP, ADC da SDP suna ganin adadin su ya kai su tsaida wanda zai jagorance su. Kamar yadda mai magana da yawun jamiyyar LP Dokta Yunusa Tanko ya bayana.

Majalisar wakilan Najeriya (Facebook/ Majalisar wakilai)

Majalisar wakilan Najeriya (Facebook/ Majalisar wakilai)

Yunusa ya ce su yan adawa da ke shirin shigowa Majalisa, suna da akida kuma kokarin su shi ne, su tabbatar da hadin kan yan adawa domin su kafa shugabanci a majalisar, ta haka ne kawai suke ganin za su kawo wa kasa da al’ummanta cigaba.

Amma daya cikin ‘ya’yan Jamiyyar APC wanda ya ce ya fi kowa cancanta da kujerar Kakakin Majalisar Wakilan, Tajudeen Abbas, ya ce Jamiyyar APC mai mulki tana kokarin daukan mataki wajen hana ‘yan adawa samun yadda suke so.

Tajudeen ya ce su ‘ya’yan Jamiyyar APC sun yi taro da Kakakin Majalisar mai barin gado akan matakin da za su dauka na tabbatar da cewa APC ta cigaba da rinjaye tare da jagorantar Majalisar Wakilan na tsawon shekaru 4 masu zuwa.

Senatoci Da Yan Majalisa Sun Gana Da Hukumar Zaben Kasa

Senatoci Da Yan Majalisa Sun Gana Da Hukumar Zaben Kasa

Tajudeen ya kara da cewa baya ga taro da suka yi da Kakakin Majalisar wakilai, su kansu yan takarar kujerar suna ta taruka domin su tsayar da mutum daya, amma sai uwar jamiyya ta baiyana shiyar da za a kai mukamin kakakin majalisar wakilan.

Wani abin dubawa shi ne batun Muslim-Muslim, da tasirin da hakan zai yi a zaben shugabanin majalisar.

Mai nazari a al’amuran yau da kullum Komred Isa Tijjani, ya ce ba a amfani da addini ko kabilanci a Majalisar Kasa.

Tijjani ya ce majalisar kasa ita ce Najeriya, ba a kawo banbancin addini ko kabilanci a Majalisar dokokin kasa. A cewar Tijjani a zamanin Shugaba Olusegun Obasanjo an yi abin da za a iya cewa tikitin Krista, domin Obasanjo Krista ne, Shugaban Majalisar Dattawa David Mark krista ne, mataimakinsa Ike Ekwerenmadu krista ne, Kakakin Majalisar Wakilai Patricia Ette krista ce.

Senatoci Da Yan Majalisa Sun Gana Da Hukumar Zaben Kasa

Senatoci Da Yan Majalisa Sun Gana Da Hukumar Zaben Kasa

Tijani ya ce Majalisa kasar ce dungurungun, ba a batun banbanci a wannan wuri tunda kowa yana nan.

Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya nan da kusan watanni biyu, lokacin da za a rantsar da yan majalisar dokokin kasar.

Ga rahoton Medina Dauda Muryar Amurka Daga Abuja Najeriya:Source link


Like it? Share with your friends!

1

You may also like