Da Gangan Gwamnoni Ke Kin Biyan Ma’aikatansu-Dino Melaye


 

Ba wani sabon labari ba ne batun rashin biyan ma’aikata a wasu jihohin Nijeriya amma abun da ke sabo shi ne batun makudan kudade da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta rabawa jihohin da adadinsa ya kai kimanin Naira biliyan 522 da miliyan 74 da aka samu daga bashin kasashen waje da aka biya fiye da kima.

Tun farko dai Sanata Dino Melaye ya ce gwamnatin Buhari ta rabawa jihohi makudan kudade da suka kai dalar Amurka biliyan 4.

Jihar da ta samu kaso mafi kankanci ita ce jihar Nasarawa wadda ta samu Naira biliyan 68.

Melaye ya zargi jihohin da cewa basa son kungiyoyin kwadago su san labarin domin kada su matsa lamba sai an biya bashin albashin da ma’aikatan ke bi.

A firarsa ta karshen shekara Shugaba Buhari ya nuna damuwarsa kan albashin ma’aikatan jihohi.

Ya ce jihohi 27 cikin 36 basu iya biyan albashin ma’aikatansu, musamman kananan ma’aikata, alhali kuwa da albashin suka dogara su biya kudin haya su kuma rike iyalansu.

Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa gwamnatocin baya basu alkinta rarar kudaden da kasar ta samu ba. “Ba a yi tanadin kudin ba, ba a gyara wuta ba ko hanyoyi ko kuma layin dogo”, inji Buhari. “Kullum zama a ke yi ana watanda da dukiyar jama’a. Irin wannan cin amana ba zai dore ba.”

Kwararre kan shige da ficen kudi Nuhu Usman ya ce gwamnoni basa son biyan albashin ma’aikatan ne domin suna yin amfani da su ta wata hanya daban.

Ya ce lokacin da gwamnatin tarayya ta ba jihohi tallafi ba a yi wani abu ba sai a wannan karon da Sanata Dino Melaye ya fito ya fallasa abun da gwamnatin tarayya ta rabawa jihohin.

Nufin shugaban kasa ne gwamnonin su biya ma’aikatansu kamar yadda shi ya yi a tarayya har da biyan kudin fansho na wajen watanni 18.

Wasu gwamnonin na ganin su ba zasu biya miliyoyin da ma’aikata ke binsu ba. Misali gwamnan jihar Imo cewa yayi ma’aikata su yi aikin kwana uku kawai kowane mako sauran kwanakin kuma duk su tafi gona.

Kwamishanan labaran jihar Gombe Umar Ahmed Suleiman ya ce matukar gwamna nada niyya zai iya biyan albashin ma’aikatansa kamar yadda ya ce ma’aikatan jiharsa na samun albashi kan kari.

Ya ce gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dan Kwambo babu abinda ya sa gaba da ya wuce biyan hakkin ma’aikatansa.

Da zarar ya samu kudi zai fara cire albashin ma’aikata ne.

Kungiyar kwadagon Nijeriya ta bakin Nuhu Toro ta ce za ta dauki mataki kan jihohin da suka gaza biyan albashin.

You may also like