
Asalin hoton, OTHER
Mahaifiyar lauyar da ƴan sanda suka kashe a Legas, Bolanle Raheem na cikin matsanancin alhinin kisan ɗiyarta.
Ta kuma yi bayanai da dama a lokacin da kwamishinan ƴan sanda na jihar, Abiodun Alabi ya kai mata ziyarar jaje a gidanta, ranar Talata.
Ta ce “kwamishina, wannan ba abu ne mai sauƙi ba, yarinya ce da na sha wahalar renon ta tun tana ƙarama, na sayar da lemu, babu wani abu da ban yi ba domin ganin ta je makaranta har ta zama lauya, yanzu ne ya kamata na ci moriyar wahalar da na sha, Allah ka ƙwato min hakkina.”
Ta faɗi hakan ne tana cikin damuwa yayin da mutane ke rirriƙe ta.
Wace ce Bolanle Raheem?
Asalin hoton, OTHER
Bolanle Raheem lauya ce, kuma ita ce shugabar kamfanin dillancin gidaje da filaye, wanda ake kira Croston Homes Consulting, a birnin Legas.
Haka nan wakiliya ce a Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya, sannan tana da ɗa ɗaya.
Ta yi karatu ne a jami’ar Olabisi Onabanjo University, da ke Ago Iwoye, a jihar Ogun.
Ta samu kyaututtuka da dama a ɓangaren kasuwancin gidaje sannan tana koya wa mutane yadda ake kasuwancin.
A lokacin ziyarar da ya kai wa iyalin marigayiya Bolanle, kwamishinan ƴan sanda na Legas ya tabbatar masu cewa za a yi adalci kan kisan nata.
Ya ce “wanda ya aikata wannan laifi zai fuskanci hukunci.”
Barista Bolanle Raheem ta rasa ranta ne sanadiyyar harbin da wani ɗan sanda mai muƙamin ASP ya yi mata a lokacin da take dawowa daga coci tare da iyalanta a ranar kirsimeti.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Legas ta bayyana cewa ta kama ɗan sandan inda ta miƙa shi ga ɓangaren binciken manyan laifuka domin gudanar da bincike.
Kwamishinan shari’a na jihar Legas, Moyo Onigbanjo ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da mutumin a gaban kotu bisa tuhumar sa da laifin kisan kai.