
Asalin hoton, OTHER
Tsohon kocin Super Eagles Samson Siasia ya ce ko da Najeriya ta je Qatar ba bu abunda za ta tabuka.
Siasia ya musanta ikirarin da wasu ke yi cewa irin rawar da wasu kasashe a nahiyar Afrika suka taka a gasar Najeriya ma za ta iya takata, da ace ta samu zuwa gasar ta kofin duniya.
To amma tsohon dan wasan tsakiyar, wanda ya lashe kofin nahiyar Afrika a 1994, ya ce tawagar da ta kasa cire Ghana a wasan share fage, babu abunda zata iya tabukawa a Qatar, gara ma ba ta je ba.
Kasashen Kamaru da Tunisia sun taka rawar gani duk da basu samu tsallakewa zagayen yan 16 ba, inda Kamaru ta doke Brazil, Tunisia kuwa ta ci Faransa.
Uwa uba kasashen Senegal da Maroko, wadanda suka kai zagayen yan 16.
Maroko ma ta kafa tarihin kaiwa zagayen kusa da karshe, wani abu da wata kasar Larabawa ko Afrika bata taba yi ba a tarihiN gasar kofin duniya.
”Da munga wulakanci a gasar kofin duniya, don za a muna cin da zai girgiza mu”, in ji Siasia.
Ya kara da cewa ” ba bu abunda Super Eagles za ta je ta yi a a gasar kofin duniya, kuma gaza cire Ghana a wasan share fage ya ishi misali.”
Siasia na cikin tawagar da ta ci wa Super Eagles kofin nahiyar Afrika a gasar Tunisia 94, da kuma zinari a gasar Olympics da aka yi a Amurka ta Atlanta 96.