Da Nine Shugaban Kasa da Tuni BokoHaram Sun Zama Tarihi – Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi ikirarin da shine shugaban kasa, Boko Haram ba su isa su yi tasiri ba. 

“Idan za ku iya tunawa lokacin muna mulki a 2002, an samu wata yar karamar kungiyar tayar da kayar baya, makamanciyar irin wannan Boko Haram, a jihar Yobe cikin kankanin lokaci muka tarwatsa su. Ba mu kara jin labarin su ba sai bayan mun bar gwamnati”.

Atiku ya yi wannan bayanin ne a yayin raba tallafi ga ‘yan gudun Hijira a garin Yola da ke jihar Adamawa.

You may also like