Da Sauran Aiki A Bangaren Yaki Da Rashawa A Najeriya – Jakadan Kasar IngilaJakadan kasar Ingla zuwa Najeriya, Paul Arkwright, yace duk da cewa ana iyakar kokari wajen yaki da rashawan shugaba Muhammadu Buhari, da sauran Najeriya.

Ya bayyana wannan ne yayinda yake jawabi ga manema labarai bayan ya gabatar da wani jawabi akan yaki da rashawa a Landan domin gano dalilan da yasa akwai wasu rashawa da ke wuyan yaka.

Yace: “ Gwamnatin Najeriya na abin da ya kamata ta hanyar izina ga cewa ba za’a amince da rashawa ba. 

“Tana tattaunawa da da kasashe harda kasa ta akan dawo da kudaden kasar da aka sace. 

Kana kuma tana kokarin wajen bayyanawa jama’ a, amma duk da haka, akwai sauran aiki.”

“Kasar Ingila na shirin hada kai da shugaba Buhari wajen dakile rashawa.”

You may also like