Da wuya a samu maganin cutar kansa a nan kusa – Bincike...

Asalin hoton, FRANCIS CRICK INSTITUTE

Wani gagarumin nazari da aka gudanar ya nuna yadda kusan daga yanzu, har abada, cutar kansa za ta ci gaba da rikiɗa domin ci gaba da ɓarna a jikin ɗan adam, in ji masana kimiyya.

Sakamakon nazarin da aka gudanar ta hanyar bibiyar cutukan kansa na tsawon shekara tara, ya bai wa masu bincike mamaki da tsoro kan irin jan aikin da ke gabansu.

A ƙarshe sun yi ittifakin cewa kamata ya yi a mayar da hankali kan hanyoyin kare kai daga cutyar, ganin cewa da wuya a iya samo maganin cutar a nan kusa.

Cibiyar Bincike kan cutar kansa da ke Birtaniya ta ce gano cutar da wuri na da matuƙar muhimmanci.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like