Daga Bakin Mai Ita shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun taurari da mawaƙan fina-finan Hausa da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood kan abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.
A wannan kashi na 128, mun tattauna da Muhammad Aliyu Inuwa wanda aka fi sani da Goga a shirin fim mai dogon zango, Dadin Kowa.