Daga Pele muka koyi ƙwallon da har ta sa muka shahara – Tijjani Babangida



.

Al’ummar duniya na ci gaba da jimamin mutuwar fitaccen ɗan ƙwallon duniyar nan, Pele wanda ya mutu yana da shekara 82.

Ana ganin Pele wanda ya mutu ranar Alhamis, a matsayin ɗan ƙwallon da ba a taɓa samun irinsa ba a duniya, kuma sau uku yana taimaka wa Brazil wajen lashe Gasar cin Kofin Duniya.

Tijjani Babangida, ɗaya daga cikin tsoffin gwarazan ‘yan ƙwallon Afirka kuma tsohon ɗan wasan Super Eagles ta Najeriya ya shaida wa BBC cewa mutuwar Pele babban rashi ne ga duniyar ƙwallon ƙafa, ba kaɗai ga Brazil ba.

A cewarsa, “mutuwar Pele ta taɓa duk wani mai sha’awar ƙwallo da wanda ke sha’awar abubuwan da Pele ya yi” a lokacin da yake raye.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like