Daga Zauren Fiqhu: Abubuwan Da Suke Tauye Albarkar Dukiya



Kasancewar ‘Yan kasuwa da yawa suna yawan rubutp tambayoyinsu zuwa ga Zauren Fiqhu akan wai dukiyarsu tana lalacewa, Jarinsu yana rushewa, shi yasa naga ya kamata in miko ‘Yar nasiha takaitacciya wacce zata kunshi gargadi game da wasu daga cikin abubuwan dake kawo rashin albarkar dukiya.

Abubuwan dake kawo ma mutum rashin albarkar dukiya suna nan da yawa. Amma ga wasu nan daga ciki domin ka kiyaye :

1. Rashin fidda hakkin Allah na wajibi, wato Zakkah. Mutukar mutum ba ya fidda zakkar dukiyarsa, to sai yayi ta fama da asara da rashin albarkar abinda ya tara. 

2. Rashin kyautata ma mahaifa : Mutukar kana da wadata amma baka kyautata ma mahaifanka, to dukiyar ba zatayi albarka ba. 

3. Rashin kula da Zumunci : Manzon Allah (saww) yace “Duk wanda yake so ajinkirta masa cikin kwanakinsa kuma a yalwata masa cikin arzikinsa, to ya rika sadar da zumuncinsa”.

Ashe kenan duk wanda ya watsar da zumuncinsa zai iya haduwa da rariyar hannu. 

4. Rashin yin sadaqah ko Kyauta ko ciyar da dukiya domin Allah : Sadaqah takan sanya dukiya ta ninninka kuma tayi albarka. Hakanan yin kyauta ga Ma’abota kusanci shima babban ginshiki ne wajen albarkar dukiya. 

5. Yin rantsuwa acikin ciniki : Mutukar Dan Kasuwa zai rika yin rantse-rantse acikin kasuwancinsa tp sai Allah ya tauye albarkar dukiyarsa. Kamar yadda yazo cikin hadisi. 

6. Tauye Hakkin Wadanda ke Qasa dakai : Mutukar zaka rika tauye hakkin yaranka na kasuwa ko iyalanka, Ko wulakantar da Musulmai, to tabbas arziki ba zai yi albarka ba. Ko kayi gaba sai ka dawo ba. 

7. Aikata Manyan Kaba’irori : Irin su Zina, Luwadi, Cin kudin ruwa, Tsafi, Chamfi, da sauransu. Duk mai yinsu ba zai ga albarkar abin hannunsa ba. Har sai ya tuba ya dena.

8. Qarancin Istighfari : Rashin yawaita istighfari da Salatin Annabi (saww) shima yana kawo ma mutum rashin albarkar dukiya. Amma idan ka yawaitasu sai kaga budi ya samu, Arziki kuma ya yawaita. 

9. Wulakanta Sallah : Mutukar dan kasuwa zai rika wulakantar da addini don neman dukiyarsa, to tabbas dukiyar ba zatayi albarka ba. Har sai ya tuba ya dena

10. Rashin tattali : Tattali ba tare da rowa ko Kwauro ba, shima yakan janyo albarkar dukiya. Kuma rashinsa yakan janyo ma dukiya lalacewa. 

11. TSAWWALA MA TALAKAWA : Da yawa daga cikin ‘Yan kasuwarmu sukan tsawwala ma dukiyarsu farashi don kwadayin samun riba. Kuma basu yin la’akari da halin da al’ummah zasu shiga. To irin wadannan ‘Yan kasuwan sukan hadu da lalacewar dukiya da kuma Mummunan karshe idan har basu tuba ba. 
Anan zan tsaya da fatan Allah yasa wadanda akayi dominsu sunji kuma sun gyara. Allah yasa haka ameen. 

You may also like