Daga Zauren Fiqhu: Nana Fatima ‘Yar Ma’aikin Allah


Assalamu alaikum Mata!!! Ku daure ku cije kuyi kokari Kuyi koyi da halaye irin na NANA FATIMA (Allah shi Qara mata aminci da yarda).

Nana Fatimah ‘yar Ma’aikin Allah (saww) Duk cikin mataye babu kamarta. Ta taso acikin gidan Annabci..

Mahaifiyarta WALIYYIYA SIDDIQIYA,  Mahaifinta kuma Shugaban Annabawa kuma Jagoran Manzanni, kuma Limamin Mala’iku (saww).

Ku dubi irin wahalar da Ma’aikin Allah (saww) yasha azamansa na Makkah amma Sayyidah Fatimah tana tayashi isar da Aiken Allah. tana kwantar masa da hankali kamar yadda ta gani awajen Mahaifiyarta.

Idan kafirai sun cutar da Mahaifinta, takan fito tayi bakin Qokarinta wajen kareshi.

Ba ayi aurenta ba sai da ta cika ‘yar Shekara 15 aduniya. Amma saboda tsantsar Ladabi bata zabi miji da kanta ba.

Mahaifinta ne ya daura aurenta ya bama Qaninsa wato ‘Dan Baffansa, (Sayyiduna Aliyu r.a).

A kyawun zubin halitta da kyawun halaye, ta zarce dukkan mataye. Ga kuma girman matsayinta agun Allah da Manzonsa Amma duk wannan bai sa tayi girman kai ko rashin biyayya ga mijinta ba. Bata taba saba masa ba.

Idan ma wani abu ya faru na rashin fahimta irin na mutuntaka, bata samun hutu acikin ranta har sai ta hakurkurtar da Mijinta.

Ku dubi matsayin Mahaifinta da kuma matsayinta agun mahaifin nata, amma duk da haka NANA FATIMAH da kanta take aikin gida. Shara, daka, Wanke-wanke, nika, da sauransu duk ita take yi da kanta.

Ta rayu shekaru 8 ko 9 tare da mijinta mai albarka.

Da ma an daura auren ne acikin shekara ta 2 bayan Hijira, Wato bayan an dawo daga yakin badar kenan. Kuma ta rasu ashekara ta 11 bayan hijira Wato Tayi Shekara 8 da wasu watanni kenan agidan mijinta.

Ta rasu bayan rasuwar mahaifinta da wata 6. Da zata rasu, ita tayi ma Kanta wankan gawa, sannan Allah ya karbi kwananta.

Awata ruwayar kuma Mijinta ne ya wanketa (ra).

Sayyidah Fatimah Shugabar Matayen Talikai.. Kuma mafi soyuwar mutane awajen Mahaifinta.

Tafi kowa yin kamanni da Mahaifinta (saww). Tafiyarsu iri daya, zamansu da tashinsu iri daya, Maganarsu ma iri daya.

Mahaifinta (saww) yace Fatimah tsokar jikina ce. Duk abinda ya fusata ta, to nima ya fusata ni.

Kuma yace: “Allah yana fushi da Fushin Fatimah”.

Allah ya girmama Nana Fatimah, don haka shima yana girmamata. Idan yana zaune idan ya hangota ta taho sai ya mike ya tarota. Yakan  rungumeta yana cewa “Madalla da ‘yata kuma sanyin idanu na”.

Duk sanda Ma’aiki (saww) ya fito sallar asuba sai ya bi ta gidanta ya tasheta. Yana cewa 
“Ku tashi izuwa sallah yaku Iyalan gidan Manzon Allah! Allah yana nufin ka’dai ya tafiyar da dukkan dau’da daga gareku ne,  kuma ya tsarkakeku mutukar tsarkakewa.

Idan Ma’aiki (saww) zai tafi yaki sai yabi ta gidanta yai mata Sallama. Sannan idan ya dawo ma haka.

Acikin iyalan gidansa ita ce farkon wacce ta fara rasuwa abayansa, kuma ita ce wacce zata fara haduwa dashi aranar Alkiyamah.

Aranar Alqiyamah idan dukkan Mutane da Aljanu da Mala’iku sun hadu, za’a ji wata murya tana cewa :
“KUYI QAS DA KANKU (KUYI LADABI) FATIMAH CE ‘YAR ANNABI MUHAMMADU (SAWW) ZATA WUCE!!!”.

Ya Allah ka bamu albarkar Nana Fatimah, Ka Qara mana Son Nana Fatimah, Ka amintar damu acikin amincinta, Ka yarda damu dominta. (aminci da yardar Allah su Qara tabbata agareta da mahaifinta). 

Salatin Allah da amincinsa su Qara tabbata abisa Shugaban Manzanni tare da iyalen gidansa da dukkan Sahabbansa.

You may also like