Daga Zauren FIQHU: Rahoton Juma’a 


Watarana Manzon Allah (saww) ya fita wani Qauyen garin Madeenah tare da Sayyiduna Zaidu bn Arqam (rta) sai suka tarar da tarkon wani Balaraben Qauye ya kama wata Barewa.

Ita barewar tana ganin Manzon Allah (saww) sai tace masa : “YA RASULALLAHI kaga wannan Balaraben Qauyen ya farautoni. Kumq ina da ‘Yan yara Qanana. Shi bai yankani na huta ba, kuma shi bai kyaleni na koma wajen yarana na shayar dasu ba”.

Sai Manzon Allah (saww) ya tambayeta “SHIN IDAN NA SAKEKI (KIJE KI SHAYAR DASU) ZAKI DAWO?”.

Sai tace “kwarai kuwa YA RASULALLAHI.. Ida  ban dawo ba Allah ya azabtar dani irin azabar rakuma mai nakuda”.

Saboda haka da Manzon Allah (saww) ya kunceta daga tarkon, nan da nan taje ta shayar da ‘ya’yanta ta dawo.

Manzon Allah (saww) ya mayar da ita cikin tarkon kenan sai ga Balaraben Qauyen yazo. Sai Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) yace masa: 

“SHIN ZAKA SAYAR MIN DA ITA?”.

Sai yace “Na bar maka ita Ya Rasulallahi”.

Sai Manzon Allah (sallallahu alaihi wa alihi wa sallam) ya kunceta ta ci gaba da rayuwarta tare da ‘ya’yanta”.

Hadisi ne Sahihi. aduba cikin:

DALA’ILUN NUBUWWA ta Baihaqee: mujalladi na 6, shafi na 334, dana 34-35.
DALA’ILUN NUBUWWA na Abu Nu’aym: Shafi na 320.

You may also like