Dajin Sambisa Ya Yi Mana Girma – Sojin Nijeriya


 

Rundunar Sojin Sama na Nijeriya ta bayarda dalilin da ya sa har yanzu ta kasa ceto ‘yan matan Chibok. A wata hira da kafar yada labarai ta BBc ta yi da Babban Hafsan rundunar, Air Marshal Sadik Baba Abubakar, ya bayyana cewa girman da dajin nan na Sambisa yake da shi, shi ya sa jiragen su ba sa iya yin shawagi a ko’ina.

Ya ce dajin na sambisa ya kai girman murabba’i dubu 60, wannan ya sa ba zai yi wu ba ace jiragen da rundunar take da su, su iya karade duk wani lungu da sako na dajin.

Ya kuma ce amma wannan bai hana rundunar yin shawagi na fiye da awanni 1260 a dajin tun farkon shekarar nan.

A fadarsa, duk da cewa har yanzu ba su samu damar ceto ‘yan matan na Chibok ba, da ma sauran ‘yan Nijeriya, rundunar ba ta bari ‘yan Boko Haram din su kai farmaki wasu garuruwan domin kama wasu mutanen da za su yi garkuwa da su.

You may also like