Dakarun Turkiyya na ci gaba da kai hare-hare a arewacin kasar Siriya karkashin shirin “Tsarn Firat” inda a ranar Talatar nan suka kashe dan ta’addar daesh 1 tare da kai wa kungiyar hare-hare sau 57.
An shiga rana ta 35 da dakarun Turkiyya suka fara kai hari a kasar ta Siriya.
Kungiyar ta Daesh ta kai wa sojin Turkiyya hari da wani jirgin sama mara matuki wanda ba kowacce kasa ce ta ke da irin sa ba inda suka jikkata sojoji 3.
‘Yan adawa a kasar ta Siriya kuma na ci gaba da kara kunna kai zuwa kudancin kasar.
Dakarun Turkiyya kuma na ci gaba da bayar da taimako ga ‘yan adawar.
Tun farkon fara kai hare-haren na Firat zuwa yau an jefa bam sau dubu 5,091 a wurare dubu 1,337.
An kai wa Daesh hare-haren da bam din HGK-1 da Kit-1.
Wannan ne karo na farko da aka fitar da bam na Turkiyya a kafafan yada labarai.
An jefa bama-baman a Tall Ar, Amiriyyah da Al-Ayubiyyah.
A harin da sojojin kawancen kasashen duniya suka kai kuma sun kashe wani dan ta’addar Daesh 1.