An Dakatar Da Alkalai 7 Da Ake Zargi Da Rashawa Da Cin Hanci A Nijeriya


 

 

 

Hukuma mai kula da da lamurran shari’a a Nijeriya (NJC) ta sanar da dakatar da wasu manyan alkalai 7 daga gudanar da aikinsu na alkalanci biyo bayan zargin da hukumar tsaron farin kaya na kasar (DSS) ta yi musu na karbar rashawa da cin hanci a yayin gudanar da ayyukansu.

Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar wannan labarin dai yana  kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan watsa labarai na hukumar Soji Oye ya fitar a karshen wani taron da hukumar ta gudanar a Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya inda hukumar ta ce an dakatar da alkalan su bakawai  har sai an kammala yi musu shari’a kan wannan zargi na rashawa da cin hanci da hukumar  DSS din ke musu.

A kwanakin baya ne dai jami’an hukumar ta DSS suka kai samame gidajen wadannan alkalan a garuruwa daban-daban na kasar inda suka yi awun gaba da su da kuma ci gaba da tsare su bisa wannan zargi da suke musu.

Ana  ganin matakin da hukumar ta NJC ta dauka ya zo ne bayan kiraye-kirayen da Kungiyar lauyoyi ta kasar bugu da kari kan zanga-zangogin da aka ta yi na  neman a dakatar da alkalan saboda wannan abin kunya da ake zarginsu da shi.

You may also like