Dakile barayin ruwa a Najeriya


 

 

Sojojin Najeriya sun kassara shirin garkuwa da jirgin ruwa a yankin Niger Delta mai fama da tashe-tashen hankula.

Nigeria Rebellengruppen im Nigerdelta (picture-alliance/dpa)

Dakarun Najeriya sun bayyana dakile wani yunkurin garkuwa da wani jirgin ruwa a yankin Niger-Delta mai fama da tashe-tashen hankula. Kana a wani lamarin na daban an cafke masu fasa bututun man fetur guda biyar a cikin yankin, kamar yadda wani mai magana da yawun rundunar sojoji ya tabbatar a wannan Lahadi.

Cikin mako jiya an hallaka barayin gabar ruwa masu yawa lokacin musanyen wuta da sojoji, yayin da aka ceto wadanda aka yi garkuwa da su, kuma babu wanda ya samu rauni cikin mutanen da aka ceto. Najeriya tana kara yawan sojoji cikin yankin na Niger-Delta tun bayan barkewar sabbin ayyukan tsageru masu dauke da makamai.

You may also like