Ali Ndume, sanata mai wakiltar mazabar kudancin Borno a majalisar dattawa ta kasa ya ce dala biliyan $1 da ka amince a kashe domin yaƙi da Boko Haram dan cikin cokali ne, ba wasu kudi ne masu yawa ba.
Gwamnoni ne suka amince a kashe kuɗin daga cikin asusun rarar kuɗin mai domin ayi amfani da su wajen siyan makamai.
Amma kuma gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose ya koka kan batun kuɗin inda ya ce za a yi amfani da su ne wajen yaƙin zaɓen shugaban kasa Muhammad Buhari a shekarar 2019.
Ya kuma garzaya gaban kotu inda ya nemi a bashi kason jiharsa domin ya yi yaƙi da yunwa a wani abu da ya kira “Yunwa Haram”.
Lokacin da ya ziyarci fadar shugaban kasa Ndume ya ce kuɗin ya yi kadan idan aka kwatanta da ɓarnar da rikicin na Boko Haram ya haifar.
“Babu wani adadin kuɗi da za ace yayi yawa wajen samar wa da ƙasarnan tsaro,”ya ce.
Lokacin da ake tsaka da muhara kan batun kudin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi karin haske kan batun inda yace za a kashe kuɗin ne ba wai kawai a yaƙi da Boko Haram ba, har wajen sauya fasalin tsarin tsaron ƙasarnan.