Dalibar Sakandire Da Mataimakin Shugaban Makaranta Yayiwa Ciki Ta HaihuDaliba ‘yar aji biyu a makarantar sakandaren jeka ka dawo na gwamnati dake Tunga-Minna da ake zargin shugaban makarantar Malam Muhammad Muhammad da yi mata ciki ta haifi da namiji.

Yarinyar ta haihu ne a kauyen su na Injita dake karamar hukumar Munya ta Jihar Neja.
Muhammad wanda aka gabatar a gaban kotu a ranar 4/afrilu/2017, wanda cigaba da fuskantar shari’a akan zarge zarge guda biyu, na saduwa da yarinyar ta hanyar da baidace ba da yiwa daliban ciki.

Wanda ake zargin da aka tsare har na tsawon wata uku a gidan yari kafin daga bisani mai shari’a Majistiret Fatima Auna ta bada belin sa akan kudi kimanin naira miliyan daya.

Mai shari’a Auna ta baiyana cewar ” laifin da Muhammad ya aikata ya sabawa sashi na 35 da 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya da sashe na 341 da 342 na kundin manyan laifuka ( Criminal Procedure Code).

Yarinyar da abun ya faru da ita ta shaidawa manema labarai a ranar talata a garin Munya cewar ” na haifi jinjiri na miji a kauyen mu domin masu kula dani a Minna sun maidani gida watan agusta bayan abun ya faru.

Mataimakin shugaban makarantar baizo ya ganni ba ko sau daya, ina neman taimakon gwamnati da ta taimaka mani domin kula da wannan jinjiri dana haifa-inji ta.

Wannan abun tsautsayi da ya faru dani ba zai karya mun guiwa ba na burina na zama likitan jinya (Nurse), ina cike da bakin cikin kasancewa uwa adai dai wannan shekarun da nake karama, amma da yardan Allah hakan ba zai taba sa na yi kasa a guiwa ba wurin ganin na cimma nasarar mafarki na na zama likitan jinya (Nurse)- a cewar ta.

Ta shawarci ‘yan uwan ta dalibai ‘ya’ya mata da su kara maida hankali akan karatun su tare da kai rahoton duk wani yunkuri na keta masu mutuntaka ga hukumar makaranta.

A zantawar sa da manema labarai Malam Haruna Galadima maihaifin yarinyar dan kimanin shekara 65 ya baiyana cewar ” ba wani kulawa da diya na tasamu daga wannan malami da yayi mata ciki har zuwa lokacin da ta haihu, hakazalika ya bukaci gwamnati ta taimakawa ‘yarsa akan ganin ta koma makaranta tare da tabbatar da anyi mata adalci.
A lokacin da nasamu labarin anyiwa diyana ciki nayi nadamar turata makaranta, saboda malamin da ya dace shike bada tarbiyya tare da dora yara akan daidaitacciyar hanyar da zasu zama shugabannin gobe nagari, amma ace yau shike bata rayuwar ‘ya’yan mutane harda yi masu ciki, ina bukatar wannan malami da ya mayar da diya na uwa a wannan lokaci ya dauki nauyin dan da ya haifa da diyana-inji Malam Haruna.
Anata jawabin daraktan hukumar kare hakkin yara ta Jihar Neja Barista Maryam Kolo ta baiyana cewar ” hukumar su ta bukaci ma’aikatan ilimi na Jiha da ta cire wani kaso na albashin malamin domin tallafawa rayuwar yarinyar.
Barista Kolo ta bada tabbacin zasu jajirce dan ganin anyiwa yarinyar adalci tare da tabbatar da ganin ta koma makaranta dan cigaba da karatunta.

You may also like