Marigayi Yusuf Abbas, wanda ke ajin karshe a jami’ar Gwamnatin Tarayya Dake Dutsinma, a jihar Katsina ya rasu ta sanadiyyar fadawa ruwan Dam din Zobe da ke kusa da jamiar, inda suka je hutawa tare da abokansa.
Dalibin wanda dan asalin jihar Kano ne, da ke karatu a sashen ilimin sanin yanayin Duniya wato Geography. Shugabanni kungiyar Daliban Jami’ar, karkashin jagorancin Shugabanta, suka raka gawar zuwa Kano.
An yi janaizar sa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Allah Ya Jikansa Da Rahama!