Dalilan APC huɗu na neman kotu ta soke zaɓen Abba Gida-GidaG

Asalin hoton, Gawuna Media

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta shigar da ƙara gaban kotun ƙorafe-ƙorafen zaɓe, inda take ƙalubalantar nasarar Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano a zaɓen 18 ga watan Maris ɗin 2023.

Cikin ɓangarorin da jam’iyyar mai mulki ke ƙara a gaban kotun, har da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ɗan takarar da aka ayyana a matsayin wanda ya ci zaɓen gwamnan Kano, da kuma jam’iyyarsa ta NNPP.

Ta ce Abba Gida-Gida, bai ci zaɓen gwamnan Kano da halastattun ƙuri’u ba.

Mashawarcin APC ta Kano kan harkokin shari’a, Barista Abdullahi Adamu Fagge, kuma ɗaya daga cikin lauyoyin da ke wakiltar jam’iyyar ya shaida wa BBC cewa sun nemi kotu ta ayyana ɗan takarar jam’iyyarsu na APC, matsayin wanda yake da rinjayen halastattun ƙuri’u.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like