Dalilan da ke sa wasu ke kallon bidiyon batsa a bainar jama’a—BBC HausaAsalin hoton, Emma Hermansson

Bayanan hoto,
An ba wa BBC wannan hoton na wani mutum da ke kallon batsa a cikin motar bas ta haya

Bronwen Reed na zaune a ɗakin karatu, tana tsammanin za ta yi karatu kamar kowane ɗalibi, kawai sai ta ga wani mutum yana kallon fim ɗin batsa a kwamfutar ɗakin karatun.

“Na yi mamaki kuma na ji wani yam. Ban san me ya kamata na yi ba a lkacin,” kamar yadda ta shaida wa BBC.

‘Yar shekara 21 ɗin wadda mazauniyar Manchester ce a Ingila, ta zaci abu ne da zai faru sau ɗaya, amma ‘yan makonni sai ta sake ganin irin wannan abin a ɗakin karatun daga mutumin.

A kwanan nan, wani ɗan majalisa na jam’iyyar Conservative a Birtaniya ya saka daga muƙaminsa bayan ya amsa lafiin cewa ya kalli bidiyon batsa a wayarsa yayin da ake zaman majalisar.

You may also like