
‘Yan arewa na zargin ana tsangwamar ‘yan uwansu da ke kuduncin Najeriya
Gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya da aka fi sani da Northern Consensus Movement a turance, ta umarci `yayanta da ke hada-hada ko safarar kayan abinci da sauran kayan masarufi da su dakatar da kai kaya kudancin kasar.
Kungiyar ta dauki matakin ne domin nuna rashin jin dadin ta game da kisan da take zargin ana yi wa fatake `yan arewa da kuma mazauna yankin.
Shugaban gamayyar kungiyoyin, Awwal Abdullahi Aliyu, ya shaida wa BBC cewa daga farkon watan Disamba da muke ciki an kashe sama da ‘yan arewa 100, an kuma kona motoci sama da 50 a kudancin kasar.
”Wannan abin takaici ne da nuna alhini, shi ya sa muka dauki matakin, domin nuna wa ‘yan arewa cewa akwai wadanda suka damu da abin da ke faruwa, akwai wadanda za su kare mutunci da mika har da kishin halin da suke ciki.
Abin da yake damun mu shi ne, ‘yan kudancin Najeriya da ke zaune a arewa babu wanda yake tsangwamarsu, suna gudanar da harkokin kasuwanci, sun mallaki gidajen kansu, sun mallaki shaguna da gonaki, da manyan kadarori na tiriliyoyin naira, an yadda da su, an amince da su miliyoyin naira.
Amma babu dan arewan da zai ce maka yana da taki daya na fili ko shago, me ya sa ba za su zauna lafiya da na mu a can ba, sai dai su dinga bi suna kashewa da kona mana dukiya?” in ji Awwal Abdullahi.
Shekaru biyu da suka wuce, kungiyar ta dauki irin wannan matakin, amma daga baya ta janye bayan fadar shugaban kasar ta shiga tsakani.
Aka kuma tura gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello, domin kwantar da hankali da warware matsalar da daukar matakin kare aukuwar hakan nan gaba.
Sai dai Malam Awwal ya ce babu wani tasiri da shiga tsakanin da gwamna Yahya Bello ya yi.
“Na farko dai akwai alkawura da aka dauka na biyan diyyar wadanda aka kashe, shi ne abu na farko da muka buta amma har yanzu ba a biya diyyar ba.
Akwai alkawarin za a daina kashe-kashen mutanen mu, shi ma babu wani sauyi da aka gani.
Ko kwanaki biyu da suka gabata mun samu rahoton an shiga wata rigar Fulani an yi awon gaba da mutane kusan 20 har yanzu babu labarinsu, don haka abubuwa ne aka yi alkawrin za a yi amma duka ba a yi ba.”