Dalilin Da Ya Sa EFCC Ba Ta Binciken ‘Yan Jam’iyyar APC – Fadar Shugaban Kasa


wp-1478002398841.jpg

 

Mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman a kan harkokin yada Labarai Femi Adesina ya bayyana dalilin da ya sa gaggan jam’iyyar APC da wadanda ke rike da mukamin gwamnati ba sa fuskantar tuhuma akan cin hanci da rashawa kamar takwarorinsu ‘yan jam’iyyar PDP.

Yayin da ake hira da shi a wani shiri na gidan rediyo Sweet FM da ke Abeokuta, ya bayyana cewa ba’a shiga binciken ‘yan jam’yyar APC din ba saboda babu wata hujja da aka samu da ke nuna cewa sun aikata laifi.

Ya kuma Jaddada cewa sam babu wani san kai a yakin da gwamnatin take yi da cn hanci da rashawa.

A fadarsa, dan wani ‘dan PDP ya tsallaka zuwa APC wannan bai bashi wata kariya ba, idan har an zarge shi kuma ana da hujja, toh tabbas za’a bincike shi kamar kowa.

Yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Buhari ta lashi takobin yi dai na ta shan suka daga wajen wasu mutane musamman ‘yan janm’iyyar adawa, wadanda ke ganin ana yin yakin da su ne ba da rashawa ba.

You may also like