Dalilin Da Ya Sa Kotun Ta Ki Amincewa Da Bukatar Mika Abba Kyari Ga Hukumomin AmurkaWASHINGTON, D.C. – Abba Kyari ya musanta cewa yana da hannu a cikin abin da wata kotu da ke Amurka ta bayyana a matsayin wani gagarumin shiri na cewa ya damfari wani dan kasuwa dan kasar Qatar sama da dala miliyan daya, wanda wani fitaccen dan damfara na Najeriya da aka fi sani da “Hushpuppi ya shirya.”

Kyari ya musanta aikata laifin.

Hushpuppi

Hushpuppi

Yana gidan yari yana jiran shari’a bisa wasu tuhume-tuhume daban-daban na zargin hada baki, cin hanci da rashawa a hukumance da kuma yin katsalandan a baje koli bayan da hukumar yaki da muggan kwayoyi ta kasar ta kama shi a watan Fabrairu.

A ranar Litinin ne alkalin babbar kotun kasar, Inyang Ekwo, ya ce ba za a iya mika Kyari ba saboda wannan shari’a da ake yi a Najeriya, domin mika shi ga Amurka zai saba wa dokar kasar.

Abba Kyari

Abba Kyari

Ba mu dai samu jin ta bakin Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin kasar Abubakar Malami ba.

Kyari na daya daga cikin mutane shida da aka gurfanar da su a kan shirin zamba a shekarar da ta gabata, a cewar wata sanarwa daga ofishin mai shigar da kara na Amurka da ke tsakiyar gundumar California.

-REUTERS

You may also like