
Asalin hoton, Getty Images
Ma’aikatan jinya a Ingila da Wales da Arewacin ireland sun fara yajin aiki, kuma shi ne mafi girma da aka taɓa yi a tarihin hukumar lafiya ta Birtaniya, NHS.
Ma’aikata za su ci gaba da kula da ma’aikatan da suke buƙatar kulawar gaggawa amma dan dakatar da sauran ayyuka irin tiyata da makamantansu.
Kwalejin Koyon AIkin Jinya da Birtaniya RCN, ta ce ma’aikatan ba su da zaɓin da ya wuce tafiya yajin aikin bayan da ministoci suka ƙi a ci gaba da tattaunawar batun ƙrin albashi.
Gwamnatin Birtaniya ta ce ba za ta iya biyan buƙatar RCN ta ƙarin albashi da kashi 19 cikin 100 ba.
Janar Sakatare na RCN Pat Cullen ta yi kira ga gwamnati ta yi abin da ya dace wajen warware matsalar kafin shekarar nan ta ƙare.
Madam Cullen ta shaida wa shirin BBC Breakfast cewa yajin aikin “ya zama wani tashin hankali ga ɓangaren aikin jinya”.
“Akwai buƙatar mu taimaki fannin lafiyar, akwai buƙatar lalubo hanyar warware matsalolin fiye da mutum miliyan bakwai da ke jira, yaya za mu yi da su?
Ta ƙara da cewa idan dai har ana son ma’aikatan jinya su dinga kula da marasa lafiya yadda ya kamata, to hakan ba zai yiwu da gurbin ma’aikata 50,000 da ba a cike ba, kuma kullum ƙaruwa gurbin ke yi,” ta ce.
Yajin aikin zai shafi ma’aikatan jinya a kusan kashi daya bisa hudu na asibitoci da tawagogin al’ummu a Ingila, da dukkan asibitocin da ke Arewacin Ireland da kuma dukkan asibitocin Wales in ban da guda ɗaya.
Amma ma’aikatan jinya ba sa yajin aikin a Scotland.
A ƙarƙashin dokokin ƙungiyar ƙwadago dai, RCN na tabbatar da cewa yajin aikin na tsawon awa 12 bai shafi ayyukan gaggawa ba.
Za a ci gaba da ayyukan gashi ga masu cutar kansa da wankin ƙoda, sannan sashen ƴan hatsari da na ba da kulawar gaggawa da na kula da jarirai sabbin haihuwa masu lalura duk za su ci gaba da aiki.
Baya ga haka, ya rage ga hukumar NHS ta buƙaci neman sasantawa kan hakan.
Babbar illar da yajin aikin zai yi shi ne ga masu zaɓar ranar da za a yi musu aiki kamar na tiyatar mazakuta da na kwankwaso da masu ganin likita yau da gobe.
NHS ta ce yana da muhimmanci mutane su ci gaba da zuwqa sashen kulawar gaggawa duk da yajin aikin.
Asalin hoton, Getty Images
“Ma’aikatan jinya sun gaji – ba a biyanmu da kyau kuma ba a ɗaukar mu da daraja,” kamar yadda wata nas daga Arewacin Ireland Lyndsay Thompson ta ce.
“E, wannan batu ne na albashi amma kuma ya haɗa da batun kula da lafiyar mutane.
“Maganar gaza ɗaukar isassun ma’aikatan jinya ma na nuna cewa rayuwar marasa lafiya na cikin haɗari.”
Madam Thompson, wacce ta shafe shekara 12 tana aiki a matsayin malamar jinya, ta ce abokan aikinta “sam ba sa son tafiya yajin aiki” amma suna ganin ɗaukar matakin ne zai kare hukumar NHS” bayan da aka shafe lokaci ba a yi ƙarin albashi ba duk da yanayin hauhawar farashi da ake ciki.
“Kawai mun ga ba mu da sauran zaɓi sai hakan saboda gwamnati ta ƙi sauraron mu,” in ji ta.
Kwalejin RCN ta ji ra’ayoyin fiye da ma’aikatan jinya 300,000 a faɗin hukumar NHS maimakon jin ta bakin ɗaiɗaikun mutane.
Hakan na nufin wasu ma’aikatan jinyar ba sa son tafiya yajin aikin, saboda waɗanda suka goyi baya ba su da yawa.
Za a sake tafiya zagaye na biyu na yajin aikin ranar 20 ga watan Disamba idan har ba a warware taƙaddamar ba.
Ta yaya yajin aikin zai shafi marasa lafiya?
Duk wanda ke cikin halin tsananin rashin lafiya ko ya ji rauni ko waɗanda rayuwarsu ke cikin haɗari, to za su iya kiran lambar 999 kamar yadda aka saba, ko kuma su kira lambar 111 ga sauran al’amuran da ba na gaggawa ba sosai, kamar maganin cutar kansa da masu matsalar ƙwaƙwalwa.
Sai dai yajin aikin zai kawo tsaiko ga sauran fannoni kamar na ganin likita na yau da gobe da tiyatar da ba ta gaggawa ba da sauran su.
Tuni a Ingila da Wales wasu ma’aikatan hukumar NHS suka samu ƙarin albashi zuwa fan 1,400 a bana – wanda ya ƙaru da kashi 4 cikin 100 na abin da ma’aikatan jinyar ke samu.