Rabi’u Musa Kwankwaso, shugaban jam’iyyar NNPP kuma dan takarar mukamin shugaban kasa a babban zaben da ke tafe a watan Fabarairu, ya tattauna da BBC kan wasu muhimman batutuwa, cii har da dalilinsa na kin mara wa Peter Obi – dan takarar mukamin shugaban kasa a jam’iyyar Labour baya.
Kwankwaso ya ce ya fi Mista Obi kwarewa, “Na yi ayyuka iri-iri; na yi aikin gwamnati shekara 17, shi bai yi ba, Na zama mataimakin kakakin majalisar wakilai, shi bai yi ba. Ko iliminmu ma idan ka duba, za ka ga ba iri daya ba ne”.