Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Suka Harzuka Da Buhari Kan Kudaden Makamai – Saraki


Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya bayyana cewa mafi yawan sanatoci ba su ji dadin yadda Shugaba Buhari ya yi gaban kansa wajen amincewa da kashe sama da Naira Bilyan 360 don sayo makamai ba tare da tuntubar majalisar tarayya ba.

Saraki ya jaddada cewa, majalisar tana goyon bayan matakin sayo makaman don yaki da ayyukan ta’addanci amma kuma yadda bangaren gwamnati ya yi watsi da bangaren majalisa shi ne bai dace ba. Tun da farko dai, bayan amincewa da kashe kudaden, Buhari ya nuna cewa zai sanar da majalisa kan wannan mataki da ya dauka.

You may also like