Dalilin da ya sa za mu fara kamen ‘yan mata masu talla a Kano – HisbahDakarun Hisbah a Kano

Asalin hoton, Mujallar Hisbah

Bayanan hoto,

An ƙirƙiri rundunar Hisbah a Kano don tabbatar da bin dokokin Musulunci

Hukumar Hisbah a Kano da ke arewacin Najeriya ta bayyana dalilan da suka sa za ta fara kama wasu ‘yan matan da ke tallace-tallace a kan titunan jihar bayan faɗuwar rana.

A ranar Laraba ne Hisba ta ba da sanarwar fara kamen tana mai cewa bincikenta ya nuna cewa da yawan ‘yan matan kan ɓige da karuwanci a cikin birnin da zarar dare ya yi.

Gwamnatin Kano ta ƙirƙiri rundunar Hisbah ne da zimmar kawar abin da ta kira baɗala da kuma tabbatar da mazauna jihar, waɗanda akasarinsu Musulmai ne, sun bi dokokin Shari’ar Musulunci.

Cikin ayyukanta har da hana shan giya, da kame matasa masu yin aski irin na mawaƙan Turawa ko kuma yin kitso da sauransu.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like