Dalilin Da Yasa Bazan Dawo Yanzu Ba – Buhari Shugaban kasa Muhammad Buhari,ya jaddada cewa likitocinsa ne kadai za su iya yanke hukunci kan lokacin da zai dawo gida Najeriya daga kasar Birtaniya inda yake jiya tun ranar 7 ga watan Mayu.

A cewarsa akwai cigaba sosai a lafiyarsa kuma yana fatan dawowa gida.

Ya Karfafa cewa ” Yanzu na koyi bin umarnin likitoci na ,mai makon ace ni nake bada umarnin. Anan sune suke bada umarnin gaba daya.”

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina, a wata sanarwa yace Buhari yayi magana a ranar Asabar lokacin da yake karbar tawagar yada jami’an labaransa da kuma babbar mai taimakasa kan harkokin kasashen waje a gidan da yake jiya a birnin dake birnin London .

Tawagar masu ziyarar sun samu jagorancin ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad, sauran sun hada da ; Femi Adesina mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu,babban mai taimakawa shugaban kasar kan harkokin yada labarai,  Lauretta Onochie babbar mai taimakawa shugaban kasar kan kafafen sadarwa zamani da kuma mai taimakawa shugaban kasar kan  al’amuran da suka shafi kasashen  waje, Abike Dabiri-Erewa.

Adesina yace tawagar ta bayyana jin dadinta kan yadda shugaban ya samu lafiya sosai. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like