Dalilin da yasa Buhari bai jagoranci zaman majalisar zartarwa ta ƙasa ba


alhaji-lai-mohammed

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bai halacci zaman mako-mako na majalisar zartarwa ta ƙasa ba saboda yana gudanar da wasu aiyuka.
Ministan yaɗa labarai Lai Muhammad ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da ƴan jaridu.
Taron wanda ya gudana a ɗakin taron majalisar dake fadar shugaban ƙasa a ranar Laraba, ya samu jagorancin shugaba Yemi Osinbajo bayan da Buhari ya gaza bayyana a wurin taron.
Rashin bayyanar shugaban ƙasar yasa anfara raɗe-raɗe raɗin cewa ya sake kwantawa rashin lafiya.
Da yake jawabi ga ƴan jaridun dake fadar shugaban ƙasa Lai Muhammad yace “Shugaban kasa bai sake kwantawa rashin lafiya ba”
Ministan ya ƙara da cewa shugaban ƙasa yana gari,kawai dai yana gudanar da wasu aiyuka.Da yaduba abin da za a tattauna a taron shine ya umarci Osinbajo da ya jagoranci zaman,wannan ai ba abu bane da ba’a saba gani ba.

You may also like