Dalilin da yasa muka canza solon yaki da Boko Haram – Burutai 


Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, ya ce dalilin da ya sa aka sauya taken yaki da kungiyar Boko Haram daga “Operation Zaman Lafiya” zuwa Operation “Zaman Lafiya Dole” shi ne domin su sauya tunanin dakarunsu a yakin da su ke yi.
An dai nada Buratai ne a shekarar da ta gabata bayan da jam’iyar APC da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta ta samu nasara a zaben da aka yi a bara.

Shugaba Buhari ya gaji yaki da kungiyar ta Boko Haram ne daga tsohon shugaba Goodluck Jonathan, wanda shima ya gada daga marigayi tsohon shugaba Umaru Musa ‘Yar adua.

Rikicin na Boko Haram ya samo asali ne tun daga shekarar 2009, ya kuma yi sanadin mutuwar sama da mutane dubu 20, sannan ya raba kusan mutane miliyan biyu da gidajensu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like