Dalilin Da Yasa Na Soki Buhari – Aisha Buhari


Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta bayyana cewa ta soki salon mulkin mijinta, Shugaba Buhari ne kwanaki saboda adalcinta da kuma tarbiyyan da aka yi mata na tsayawa kan gaskiya a kowane lokaci.

Uwargidan Shugaban ta yi wannan ikirarin ne a lokacin da ta amince da lambar yabon da kamfanin buga jaridar ‘ Vanguard’ ya ba ta inda ta nuna cewa ba ta yi nufin kaskantar da mijinta kan kalamanta amma ta jaddada cewa za ta mara masa baya a zabe na gaba.

Kwanakin baya ne dai, Uwargidan Shugaban kasar ta ta yi hira da BBC inda ta yi barazanar cewa ba za ta sake binsa wajen yakin neman zabe ba idan har ya yanke shawarar yin tazarce kan abin da ta kira rashin adalcin da ake tafkawa a cikin gwamnatin.

You may also like