Dalilin da yasa zan sake tsayawa takara -Buhari


A jiya ne shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa na shekarar 2019.

Ana ganin hakan ka iya sawa ya zama dantakara daya tilo a jam’iyar APC mai mulki.

Shugaban ya bayyana aniyarsa ya yin wani taron sirri na shugabannin jam’iyyar APC da ya gudana jiya a Abuja.

Buhari ya bayyana cewa ya yanke shawarar sake tsayawa takara ne domin amsa kiraye-kirayen da miliyoyin yan Najeriya ke yi masa na ya sake tsayawa takara a kakar zaben 2019.

An dade ana ta kiraye-kirayen shugaban da ya bayyana ra’ayinsa kan batun sake tsayawa takararsa.

Duk da shiru da shugaban ya yi kan batun takararsa,ya sha yin jurwaye me kamar wanka  kan batun takarar ta sa a lokacin da yake ziyarar aiki a wasu jihohi.

A jihar Benue lokacin da ya kai ziyarar jajen mutanen da suka mutu a rikicin fulani makiyaya da manoma shugaban ya ce “watakila zan dawo jihar Benue yakin neman zabe”.

Saboda haka sanarwar ta jiya da shugaban kasar ya yi ba ta zo wa mutane da mamaki ba.

You may also like