Dalilin Sauke Shugabannin Kananan Hukumomin Neja – Majalisa


Majalisar dokokin jihar Neja ta tabbatar da matakin Gwamnatin jihar na sauke shugabannin kananan hukumomin bisa rashin tabuka komai tare kuma da karkatar da kudaden jama’a.

Haka ma, majalisar ta ba Gwamnan jihar Umanin gudanar da sabon zaben kananan hukumomi a tsakanin watanni uku masu zuwa. Kwanaki ne dai, wata kotun tarayya ta hana Gwamantin jihar sauke shugabannin kananan hukumomi bisa hujjar cewa wa’adinsu na shekaru uku ba su cika ba.

You may also like