Dalilinmu na watsi da buƙatar Buhari bayan ranto tirliyoyin naira daga CBN – Majalisar Dattijai.

Asalin hoton, Getty Images

Majalisar Dattijan Najeriya ta yi watsi da buƙatar Shugaba Muhammad Buhari ta neman amincewa da wasu maƙudan kuɗaɗe da gwamnati ta karɓa da sunan rance daga Babban Bankin ƙasar.

Maƙudan kuɗaɗen dai sun zarce naira tirliyan ashirin da biyu.

Gwamnati ta yi ta karɓar kuɗaɗen ne a matsayin rance mai gajeren zango ko buƙatar kuɗi ta gaggawa tun kafin ta samu amincewar majalisar tarayya.

An dai ta da jijiyoyin wuya yayin zaman majalisar na ranar Laraba, saboda zargin da wasu ke yi cewa akwai rashin gaskiya a cikin lamarin.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like