Dambazau ya umarci babban sifetan ‘yan sanda ya koma yankin arewa maso gabas da zama


Abdulrahman Dambazau, ministan cikin gida, ya umarc,Ibrahim Idris babban sifetan yan sandan Najeriya da kwamandan samar da tsaro ta NSCDC, Abdullahi Muhammad da su koma yankin arewa maso gabas.

Za su hada kai da sojoji da gwamnoni domin su tabbatar da cewa an samar da tsaro a makarantun da suke jihohin Yobe, Borno da kuma Adamawa.

Fadar shugaban kasa ce ta sanar da umarnin da ministan ya bayar cikin  jerin wani sakon Tweeter da fadar ta wallafa.

Dambazau ya ce makusudin umarnin shine taimakawa wajen dakatar da sake kai hari a makarantu dake yankin.

“Ministan cikin gida ya umarci babban sifetan ‘yan sanda da kwamandan NSCDC, su koma yankin arewa maso gabas da zama kana su hada kai da kwamandan “Operation Lafiya Dole”da gwamnonin Yobe, Borno da Adamawa domin tabbatar da an  tura jami’an tsaro a dukkanin makarantun dake yankin da aka kwato;daga kungiyar Boko Haram.” Ya ce

You may also like