Dan Bindiga Ya Hallaka Mutane 39 A Turkiyya


 

A kalla mutane 39 ne suka hallaka a yayin da wani dan bindiga da yayi shigar burtu ya bude wuta a wani gidan rawa dake birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

An dai kai harin ne a yayin da daruruwan Turkawan da kuma ‘yan kasashen waje ke bikin shiga sabuwar shekara Miladiya a gidan rawar na Reina.

Daga cikin dai wadanda suka hallaka har da ‘yan kasashen waje 16.

Ko baya ga wadanda suka mutun, akwai wasu sama da arba’in da suka raunana.

Gwaman yankin Vasip Sahin inda lamarin ya auku, ya shaida cewa sai da aka harbe dan sanda da kuma wani mai gadin gidan rawan daga nesa, kafin daga bisani dan bindigan ya kusa a cikin gidan rawan.

An kiyasta cewa mutane sama da 700 ne cikin gidan rawan a yayin da dan bindiga ya bude masu wuta, lamarin da yasa dayewa daga cikinsu suka yi ta fadawa cikin kogi domin tsiratar da rayukansu.

Wannan harin dai ya sa kasar ta Turkiyya ta soma sabuwar shekara cikin makoki, baya ga ire-ire harin ta’adancin data fustanta a shekara 2016 da mukayi ban kwana da ita, wadanda ake dangantawa da kungiyar ‘yan ta’addan IS ko kuma ‘yan tawayen Kurdawa.

You may also like