Dan Fashi Ya Yiwa Sama Da Mata 30 Fyade Cikin Shekaru 3Wani kasurgumin dan fashi mai shekaru 37, Lanre Olowojobi, da akafi sani da Pumpy, ya bayyana yan sanda yadda shi da mukarrabansa suke yiwa yan mata fashi da kuma aikata fyade. 

Jami’an tsaro sun kama Pumpy ne a Mushin dake jihar Legas. 

Olowojobi wanda shi da yaransa sun dade suna addabar al’ummar Mushin, ya bayyanawa yan sandan cewa ya kashe da yawa daga cikin mutanen da ya yiwa  fashi bayan da suka ki yarda ya raba su da kayayyakinsu. 

An dai kama mai laifin a karshen makon nan, yayin wani samame da yan sanda suka kai maboyar batagari dake unguwannin,  Akala, Idi-iro da kuma Fadeyi dake cikin birni.Samamen ya biyo bayan yawan korafin da mutanen gari suke yi akan aiyukan Pumpy da mukarrabansa.

A jawabin da yayiwa yan sanda Pumpy ya bayyana cewa ya yiwa yan mata sama da 30 fyade cikin Shekaru ukun da suka gabata.

Kasurgumin dan fashin ya fito ne daga jihar Ekiti, ya kuma bayyana cewa ya kashe mutane sama da  10 a fadan da sukeyi a yankin na Mushin.

Ya kara da cewa yana da kananan yara mata da maza sama 20 da suke yimasa tallan miyagun kwayoyi.

Shugaban rundunar yan sanda ta musamman dake jihar Legas Sufuritanda, Olayinka Egbeyemi,ya tabbatar da kama mai laifin,  ya kuma  ce za’a cigaba da bincike kafin a gurfanar dasu a gaban Kotu. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like