Dan Gidan gwamnan Kano Da Yake Hawa Motar $250,000 Dai Dai Da Milliyan 100 Kudin Najeriya. 


 

Yadda Dan Ganduje Ke Kece Raini Da Ruwan Nairori.

A yayin da talakawa a jihar Kano suke fama da matsanancin talauci da tsadar rayuwa. Shi kuwa Muhammad Abdullahi Umar mai shekaru 19 da haihuwa kuma da na biyu a wajen Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya cika kafafen sadarwa na zamani da hotunan tamfatsa-tamfatsan motocin alfarma na kece-raini gami da ababen more rayuwa masu dan karen tsada.


Sayayya ta kwanan nan da Muhammad Abdullahi Umar Ganduje ya yi, ita ce (Ferrari 488) wacce aka kiyasta kudin ta ya kai Dala $250,000 Dai Dai da milliyan 100 kudin Najeriya.

A cewar majiyar mu wan sa ma na da irin wannan motar da ya ajiye ta a Abuja.

An bayyana Muhammad Abdullahi Umar Ganduje ya kasance ma’abocin son kyale-kyale da suka hada da, agogon Zinare, sabbin motoci kirar Benz da Porsche.
Muhammad Abdullahi Umar Ganduje, inkiya “Kanky Lion” a shafin twitter kuma, @Lilkankz a bayyana kansa a matsayin shugaban kamfanin “CEO Avalanche Group Holdings Inc.”

 

 

cxfpasiweaakufj

 

 

 

 

 

cvech0eu8aaz1zm

 

 

 

 

 

cna8bwrwsaea5u6

You may also like