Dan Gidan Marigayi Gaddafi Ya Dau alwashin Daukar Fansar Kisan Gillar Da Aka yi Wa Baban sa Dan tsohon shugaban kasar Libiya Mu’ammar Gaddafi, Saiful Islam ya lashi takobin daukar fansar kisan wulakancin da shugabannin kasashen yamma da wasu takwarorinsu Larabawa suka yi wa mahaifinsa.

Matashin ya hana wa idanunsa barci, tun a lokacin ya fito daga gidan wakafi.

Domin buri daya tilo da ya sa a gaba shi ne tattara dukannin wasu shaidun da za su nuna wa duniya irin makarkashiya da aka kulla a wajen kashe mahaifinsa da kuma durkusar da tattalin arzikin Libiya.

Domin cimma burinsa, Saif ya dauki wani kwararren lauya wanda ke ci gaba da aiki tukuru.

Da yake magana a gaban manema labarai, lauyan Saif Gaddafi ya ce, ”Muna gaf da kai kara a kotun kasar Libiya da babban kotun kasa da kasa, domin na dauki alwashin daukar fansar kisan babana. Muna da shaidu masu dumbin yawa wadanda zai wuya ai watsi da su.

“Wadannan takardun da ke a hannunmu a yanzu haka, na nuna irin muhimmiyar rawar da wasu kasashen yamma da na Larabawa suka taka a wajen kashe mahaifina”.

Wasu makusantan mulkin marigayi Muammar Gaddafi, sun tabbatar da  cewa, a yanzu haka Saif ne kadai ke iya jagorantar Libiya da kuma hada kan ‘yan kasar.

You may also like